Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Standard Na Ingila Ya Biya Amurka Tarar Dala Milyan $340 Saboda Iran.


Wani Banki a kasar turai masu fama da matsalolin kudi.
Wani Banki a kasar turai masu fama da matsalolin kudi.

Bankin Standard Chartered na Ingila ya yarda zai biya tarar dala milyan $340 kan zargin da mahukuntan Amurka suka yi masa na boye huldar kudi tsakaninsa da Iran ko wakilanta.

Bankin Standard Chartered na Ingila ya yarda zai biya tarar dala milyan $340 kan zargin da mahukuntan Amurka suka yi masa na boye huldar kudi tsakaninsa da Iran ko wakilanta, na dala milyan dubu $250, cikin shekaru 10 da suka wuce.
Mutane suke hada hada cikin wani Banki
Mutane suke hada hada cikin wani Banki


Bankin Chartered ya musanta wan nan zargi cikin makon jiya, lokacinda wasu jami’an Amurka masu sa ido kan hada-hadar kudi suka yiwa bankin wanda shine na biyar a girma a Ingila, cewa ya zama baragurbi saboda boye mu’amalar kudi har sau dubu dari shida, tsakaninsa da kasar Farisa. Amma sai bankin yayi wuf ya daidaita da hukumomi kamin a fara zaman sauraron shaida ranar wan nan laraba.

Wasu masu sa ido hudu sun fara bincike kan bankin Standard Chartered saboda zargin hulda da Iran ko wakilanta, kuma wadan nan d a suka fara sabon binciken, basa cikin wadanda suka daidaita da Bankin.

Dokokin Amurka suna hana duk wata harkar kasuwanci da Iran. Amurka da wssu kasashen yammacin duniya suna kokarin tilastawa Tehran ta kawo karshen abinda suka kira shirin habaka makaman Nukiliya da Iran take yi. Shirin da Farisa ta sha musantawa cewa babu shi.
XS
SM
MD
LG