Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Philippines Ta Cimma Yarjejeniya Da Musulmi 'Yan Tawaye


Mayakan kungiyar "Moro Islamic Liberation Front" su na sintiri cikin wani sansaninsu a Sultan Kudarat dake kudancin kasar a 2011
Mayakan kungiyar "Moro Islamic Liberation Front" su na sintiri cikin wani sansaninsu a Sultan Kudarat dake kudancin kasar a 2011
Gwamnatin Philippines ta ce ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta wucin gadi da kungiyar 'yan tawayen Musulmi mafi girma a kudancin kasar, da nufin kawo karshen yakin aware da aka shafe shekaru arba'in ana gwabzawa, har aka yi hasarar rayuka fiye da dubu 120.

Shugaba Benigno Aquino ya fada cikin wani jawabin da yayi ta telebijin ga al'ummar kasar lahadin nan cewa yarjejeniyar da aka kulla da kungiyar "Moro Islamic Liberation Front" ko MILF a takaice, zata kirkiro da wani sabon yanki na Musulmi da za a rika kira "Bangsamoro" wanda kuma zai maye gurbin wani yankin da aka ware musu wanda ya kasa kawo karshen wannan fitina.

Za a kafa sabon yankin na Bangsamoro a lardin Mindanao mai arzikin albarkatun kasa na kudancin kasar, wanda kuma kungiyar MILF take dauka a zaman kasar kaka da kakannin al'ummarta.

Jami'ai suka ce a ranar 15 ga wannan wata na Oktoba a Manila, babban birnin kasar, za a rattaba hannu a kan wannan yarjejeniya wadda ta fayyace irin iko da hanyoyin kudaden shiga da kuma fadin wannan yanki. Suka ce idan komai ya tafi daidai, za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya kammalalliya nan da shekarar 2016, a lokacin da wa'axdin shugabanci an shekaru shida na Mr. Aquino zai kare.

Kungiyar Musulmi 'yan tawayen ta yaba da wannan yarjejeniya da aka kulla a zama na karshe na shawarwarin neman sulhu da ake gudanarwa a kasar Malaysia, a zaman harsashin zaman lafiya.

Sakatraiyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta bayyana yarjejeniyar a zaman shaida ta irin kudurin bangarorin biyu na kawo karshen wannan fitina ta hanyar lumana.
XS
SM
MD
LG