Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Taron Kolin Kasashe Masu Magana Da Faransanci


Shugaba Joseph Kabila na Kwango (hagu) da shugaba Francois Hollande na Faransa (dama) a wurin bude taron kolin a Kinshasa
Shugaba Joseph Kabila na Kwango (hagu) da shugaba Francois Hollande na Faransa (dama) a wurin bude taron kolin a Kinshasa

Tawayen gabashin KWango-ta-Kinshasa da halin da ake ciki a kasar Mali sune zasu sha gaban komai a wannan taron koli da ake yi a birnin Kinshasa.

Shugaba Francois Hollande na Faransa, ya jaddada muhimmancin kare hakkin bil Adama, tare da cimma zaman lafiya a yankunan dake fama da fitina a kasar Kwango-ta-Kinshasa. Shugaban na Faransa ya yi wannan furuci ne a lokacin bude taron kolin kasashe masu magana da harshen Faransanci, a Kinshasa, babban birnin Kwango.

A can baya, Mr. Hollande ya soki yadda ake keta hakkin bil Adama a gabashin kasar ta Kwango, inda ake fuskantar tawaye. Ya bayyana lamarin a zaman wanda ba za a amince da shi ba.

Shugaba Joseph Kabila na Kwango ya gana da Mr. Hollande tun farko a yau asabar din. A jawabinsa wajen bude taron kolin kuma, ya bayyana tawayen da ake yi a gabashin kasarsa a zaman "yaki na rashin adalci" da wasu daga waje suka dora ma kasarsa. Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kasar Rwanda da goyon bayan tawayen da ake yi a gabashin Kwango, zargin da Rwanda ta musanta.

Ana sa ran cewa wannan tawaye da ake fama da shi a Kwango-ta-Kinshasa da kuma halin da ake ciki a kasar Mali, zasu mamaye tattaunawa a wannan taron koli da za a kammala gobe lahadi.

Jiya jumma'a, Majalisar Dinkin Duniya ta zartas da kudurin da ya share fagen girka sojojin kasashen waje da zasu taimakawa gwamnatin rikon kwarya ta Mali wajen takalar 'yan tawaye masu kishin Islama wadanda suka kwace yankin arewacin kasar.
XS
SM
MD
LG