Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Shugaban Afirka Da Ya Cancanci Lambar Yabo


Mo Ibrahim, wanda ya kafa gidauniyar bayar da lambar yabo ga shugabannin Afirka da suka kyautatawa al'ummarsu, a dama
Mo Ibrahim, wanda ya kafa gidauniyar bayar da lambar yabo ga shugabannin Afirka da suka kyautatawa al'ummarsu, a dama

A karo na uku cikin shekaru hudu, Gidauniyar Mo Ibrahim ta ce babu shugaban Afirka da ya cancanci samun lambar yabonta ta iya shugabancin kwarai

Sau uku kenan cikin shekaru hudu da cibiyar Mo Ibrahim ke kin bayar da kyautar yabawa iya gudanar da shugabanci a Afirka.

Cibiyar ta yi sanarwa a birnin London a yau litinin cewa ba za ta bayar da kyautar yabon ta dola miliyan biyar ba. Ta ce daga cikin shugabannin da ta duba yiwuwar baiwa kyautar, babu wanda ya cika sharudan cancantar samun kyautar.

Cibiyar ta kan bayar da kyautar yabon ce ga wani shugaban kasar Afirka, mace ko namiji, da aka zaba ta hanyar demokradiya, wanda ya yi kyakkyawan mulki kuma ya bar shugabanci daga kammala wa'adin mulki.

Mo Ibrahim, dan kasuwar Ingila dan asalin kasar Sudan wanda ya kafa cibiyar, ya shaidawa manema labarai cewa kwamitin duba cancantar samun kyautar yabon ba ya so ya sauya ka'idojin shi na farko game da cancantar cin kyautar.

Tun da aka kafa cibiyar a shekarar 2006 sau uku kawai ta bayar da kyaututtukan yabon iya mulki a Afirka, shugaban baya-bayan nan da ya ci kyautar shi ne tsohon shugaban kasar Cape Verde Pedro Pires a shekarar 2011.

Haka kuma a yau litinin cibiyar ta gabatar da rahoton ta na shekara-shekara a kan shugabanci a Afirka. Ta ce a cikin shekaru goman da suka gabata an samu kyautatuwar shugabanci a Afirka.

Shekaru biyu kenan a jere da Mauritius ce kasar da ta fi samun kyakkyawan shugabanci a Afirka, daga ita sai Cape Verde, sannan Botswana, Seychelles da Afrika ta Kudu. Somaliya ce ta karshen karshe a jerin wadannan kasashe.
XS
SM
MD
LG