Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Ta Dauki Laifi.


Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton a Lima kasar Peru.
Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton a Lima kasar Peru.

sakatariyar harakokin wajen Amurka Clinton ta karbi laifin harin da ya halaka jakadan Amurka a kasar Libiya tare da wasu Amurkawa uku a Benghazi.

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta dauki laifin faruwar munmunan harin da aka kai karamin ofishin jakadancin Amurka a kasar Libiya a cikin watan jiya, ta ce daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan ta har da kula da tsaro da kiyaye lafiyar wadanda ke karkashin ma’aikatar harakokin wajen Amurka su na aiki a fadin duniya.

A cikin wasu hirarrakin da ta yi da gidajen talbijin a yayin wata ziyara a kasar Peru, Clinton ta fada a jiya litinin cewa babu yadda za a yi shugaba Barack Obama da mataimakin sa Joe Biden su iya sanin irin shawarwarin da jami’an tsaron da ke kula da ofishin jakadancin su ka yanke.

Haka kuma ta ce yanayin faruwar hare-hare iri na ranar 11 ga watan satumba wanda ya zama sanadin mutuwar jakadan Amurka a Libiya da wasu Amurkawa uku, wani irin yanayi ne mai wuyar ganewa a lokacin da abun ke faruwa.

Harin, da kuma yadda gwamnatin Obama ta maida martani ga abun da ya biyo baya , sun zama abun magana a yakin neman zaben shugaban kasar Amurka. Dan takarar jam’iyar Republican Mitt Romney ya soki lamirin Mr.Obama da cewa bai dauki isassun matakan tabbatar da tsaro a karamin ofishin jakadancin Amurka a Benghazi ba.

A jiya litinin Clinton ta ce, ba ta so harin ya zama wata maganar siyasar sukan juna.

Da farko gwamnatin Obama cewa ta yi, harin ya faru ne sanadiyar zanga-zangar nuna bacin rai da fim din cin mutuncin Addinin Islama da aka yi a nan Amurka, amma kuma yanzu cewa ta ke yi hari ne na ta’addanci.
XS
SM
MD
LG