Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Dora Ma Isra'ila Laifin Harin Bam Kan Masana'antar Makamai


Wuta tana ci a masana'antar makamai ta Yarmouk dake Khartoum bayan tashin wani abu a daren talata
Wuta tana ci a masana'antar makamai ta Yarmouk dake Khartoum bayan tashin wani abu a daren talata

Gwamnatin Sudan ta ce ta yi imanin jiragen yakin Isra'ila hudu ne suka kai farmaki kan masana'antar makamai ta Yarmouk dake Khartoum cikin daren talata

Gwamnatin Sudan ta dora ma Isra'ila laifin abinda ta ce harin bam ne a kan wata masana'antar makamai dake babban birnin kasar.

Ministan yada labarai na Sudan, Ahmed Belal Osman, yace yayi imani harin da wasu jiragen yaki guda hudu na kasar Isra'ila suka kai ne ya haddasa fashe-fashen da aka samu a masana'antar kere-keren makamai ta Yarmouk dake Khartoum cikin daren talata.

A wajen wani taron 'yan jarida a yau laraba, yace fararen hula biyu sun mutu a fashe-fashen, wadanda suka lalata gine-ginen dake kusa da nan, suka kuma rika cilla albarusai dake yin bindiga sama.

Rundunar sojojin Isra'ila da kuma ma'aikatar harkokin wajenta sun ki cewa uffan kan wannan.

Osman yace garewanin bama-bamai da aka gani a wurin sun nuna cewa Isra'ila ce ta kai harin. Ya bayyana wannan abinda ya kira farmaki a zaman wani yunkuri na Isra'ila na gurgunta karfin sojan kasar Sudan.

Yace Sudan tana da ikon mayar da martani, ya kuma ce watakila zata kai wannan batu gaban Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu shaidu sun fadawa wani wakilin Muryar Amurka mai suna Isma'il Kushkush cewa sun ga wasu jiragen sama guda biyu sun bi ta kan wannan masana'anta jim kadan kafin a ji karar fashe-fashen cikin daren talata.
XS
SM
MD
LG