Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Amnesty Int’l, ta ce matakan da jami’an tsaron Nijeriya ke daukawa game da kungiyar Boko Haram na dada yamutsa al’amura.
A wani sabon rahotonta da ya fito yau Alhamis, kungiyar ta Amnesty ta ce jami’an tsaron sun tafka aika-aikar cin zarafin bil’adama, ciki har da kame ba bisa ka’ida ba, da kuntatawa da kuma kashe-kashen da su ka saba wa doka.
Kungiyar ta ce, aika-aikar Boko Haram, gami da matakan da jami’an tsaron ke daukawa, sun haddasa tashe-tashen hankula masu maimaita kansu, da kuma kara firgitarwa a Nijeriya.
Salil Shetty, Sakatare-janar din kungiyar ta Amnesty a Nijeriya, ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta kare ‘yan kasar daga Boko Haram, to amman bisa tanajin doka da oda.
Rundunar Tsaron Nijeriya ta Hadin Gwiwa (JTF), ta karyata wasu rahotannin watan jiya da ke nuna cewa, sojoji sun hallaka akalla mutane 30, tare da kona shaguna da gidaje a birnin Maiduguri, a matsayin martanin wani harin bam din da aka kai masu. A bayanin da ta yi a wancan lokacin, JTF ta ce sam babu wata shaida ta kashe-kashen da su ka saba wa doka, da kuntatawa, da kone-kone da kame ba bisa ka’ida ba da hukumar ta JTF ta aikata a jihar Borno.