Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau kwana 3 da fara Zanga-zangar kin sabuwar dokar da Shugaba Morsi ya kafa a Masar


Zanga-zangar kin sabuwar dokar Shugaba Morsi
Zanga-zangar kin sabuwar dokar Shugaba Morsi
An shiga rana ta 3 a zanga-zangar da ake yi a Masar kan shawarar da Shugaba Mohammed Morsi ya yanke ta kara wa kansa dinbin iko. Dokar da Shugaban kasar ya kafa don amfanar kansa ta kare shi daga iko bangaren shari’ar kasar kuma ta kare takwarorinsa ‘yan kishin Islama da ke Majalisar Dokokin kasar.

Masu zanga-zanga a Dandalin Tahrir mai tarihi da ke birnin al-Khahira, inda nan ne cibiyar zanga-zangar 2011 da ta yi sanadin hambarar da Shugaba Hosni Mubarak, sun yi ta jifar ‘yan sanda da duwatsu a yau Lahadi. ‘Yan sandan sun mai da martani da jefe-jefen barkonon tsohuwa.

Wani fitaccen barden rajin dimokaradiyyar Masar mai suna Mohammed el-Baradei ya yi kira ga Shugaba Morsi a jiya Asabar da ya janye iko kusan mara iyakan da ya bai wa kansa.

Hukumar koli ta alkalan Masar, ita ma ta yi Allah wadai da dokar ta Morsi.
XS
SM
MD
LG