Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Morsi Na Shirin Yiwa Kasar Masar Jawabi


Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi
Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi

Shugaban kasar Masar Mohamed Morsi na shirin yiwa kasa jawabi cikin fafatawa tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga.

Shugaban kasar Masar Mohamed Morsi ya na shirin yin jawabi ga ‘yan kasa a yau alhamis, a daidai lokacin da Kiristoci da masu sassaucin ra’ayi su ka kauracewa zaman yin kuri’a kan wani daftarin kundin tsarin mulki.
Mr.Morsi ya tsawaita wa’adin rubuta kundin tsarin mulki daga Disemba zuwa Fabarairu, amma kakakin majalisar dokoki ya ce karin lokacin ba shi da wani amfani.

Misiriwa sun ci gaba da yin zanga-zangar da su ke yiwa shugaba Morsi a dandalin Tahrir a kwana na bakwai a jere, su na zargin sa da yin abubuwa kamar dan kama karya. Haka kuma an kwan dare ana fafatawa tsakanin masu zanga-zangar da ke jifa da duwatsu da ‘yan sandan da ke harba mu su gwangwanayen hayaki mai sa hawaye.

Masu zanga-zanga na rera wakokin kin jinin gwamnati a Dandalin Tahrir, birnin Alkahira
Masu zanga-zanga na rera wakokin kin jinin gwamnati a Dandalin Tahrir, birnin Alkahira
Magoya bayan shugaban kasar sun lashi takobin yin ta su zanga-zangar ranar asabar.
Manyan kotunan kasar Masar sun shiga yajin aiki daga jiya laraba a wani matakin nuna rashin yardar su da dokokin da shugaban ya kafa, kuma sun sha aradun daina aiki har sai kotun tsarin mulki ta yanke hukunci a kan dokar Mr.Morsi wadda ta ba shi kariya game da bayyana a gaban kotu.

Kotun tsarin mulki ta zargi Mr.Morsi da tasamma ‘yancin kan ta babu wani dalili.Shugaban ya ce an yi dokar ce don a kare hukumomin mulkin kasa.
XS
SM
MD
LG