Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kasar Mauritania Zai Sake Komawa Faransa


 Shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz
Shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz

Shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz zai je birnin Paris domin ya kara ganin likitoci game da raunukan da ya samu sanadiyar harbin shi a kwanakin baya

Shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz ya sake komawa kasar Faransa domin ya kara ganin likitoci sanadiyar raunukan da yayi bayan harbin shi da aka yi da bindiga a watan Oktoba.

A wani taron da yayi da manema labarai da yammacin alhamis Mr. Aziz ya ce zai yi kwana biyar zuwa goma a birnin Paris inda za a yi mi shi wasu gwaje-gwaje a asibiti.
Kasa da mako daya kenan da ya koma gida Mauritania daga kasar Faransa bayan harbin da daya daga cikin sojojin shi ya yi mi shi da bindiga a cikin watan oktoba, cikin wani al’amarin da gwamnatin kasar ta ce tsautsayi ne.

A yayin taron na manema labarai, haka kuma Mr.Aziz ya yi kashedi game da kai gudunmowar sojoji makwafciyar kasar Mali inda watanni da dama kenan da ‘yan tawaye masu alaka da al-Qaida su ka kama arewacin kasar kuma su ka kafa tsarin mulkin Shari’ar Islama.

Mr.Aziz ya ce gudunmowar sojojin kasashen wajen na iya haifar da wani munmunan abun da zai biyo baya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya ce, Mr.Aziz ya yi kashedin cewa gudunmowar sojojin kasashen waje za ta sa ‘yan yankin arewacin Mali su ji kamar barazana ake yi mu su, saboda haka sai ta yiwu su hada kai da ‘yan ta’adda a yankin.

Kungiyar kasashen Afirka da kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO sun cimma jituwa kan wani shirin tura sojoji kasar Mali.

Amma a cikin wani rahoton da babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya gabatarwa Kwamitin Sulhun Majalisar a ranar laraba, ya fada cewa da sauran wasu muhimman matsaloli game da dorewar aikin da zai sa a tura sojojin. Haka kuma babban magatakardan na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kashedin cewa rashin yin aikin da kyau sosai na iya ta’azzara halin tagayyarar bil Adama a kasar Mali kuma ya kai ga buda kafar aikata munmunan cin zalin tauye hakkokin bil Adama.
XS
SM
MD
LG