Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijirar Mali na Fuskantar Kalubalen Rashin Lafiya da Abinci


Timal Bara, 35, da diyarta Ka-Bito Bara mai shekaru 5 a sansanin gudun hijira na Mbera refugee camp a kudancin Mauritania, May 23, 2012.
Timal Bara, 35, da diyarta Ka-Bito Bara mai shekaru 5 a sansanin gudun hijira na Mbera refugee camp a kudancin Mauritania, May 23, 2012.
Kungiyar agajin kasa da akasa ta “Doctors Without Borders” ta bada rahoton cewa ‘yan gudun hijirar kasar Mali dake Mauritania na fuskantar babbar matsala wajen rashin kayan abinchi da rashin lafiyar kananan yara. Darektar kungiyar ta “Doctors Withour Borders” Karl Nawezi tace jami’an kiwon lafiyar kungiyar sun sami nasarar tallafawa ‘yan gudun hijirar da suka galabaita sama da dubu guda a yankin Mbera dake kudu maso gabshin Mauritania.


Darekta Nawezi ta ce sakamakon binciken da kungiyar ta gudanar ya nuna cewa a kowace al’ummar dake gudun hijira za’a sami yara biyar da basa samun isasshen abinchin dake gina jiki, akwai kuma kusan yara yawansu ya kai kashi 17 daga cikin dari na duk gungun ‘yan gudun hijirar dake zaune a sansanin ‘yan gudun Hijira. Akwai ‘yan gudun hijirar kasar Mali da yawansu ya kai dubu 55,000 a kowane sansanin ‘yan gudun hijirar dake Mauritania tun farkon watan na Janairun shekarar da ta gabata ta 2012.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG