Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Ake Bikin Rantsar Da Barack Obama Na Wa'adi Na Biyu


Majalisar Dokokin Amurka kennan a safiyar da ake bukin rantsar da shugaban kasa, Litinin, Junairu. 21, 2013 (AP Photo/Scott Andrews, Pool)
Majalisar Dokokin Amurka kennan a safiyar da ake bukin rantsar da shugaban kasa, Litinin, Junairu. 21, 2013 (AP Photo/Scott Andrews, Pool)
Yau litinin za’a kara rantsar da shugaban Amurka Barack Obama a bikin rantsarwa da za’a yi a gaban jama’a a bakin harabar yammacin majalisar dokokin Amurka, a inda zai yi jawabi, kafin ya taka zuwa fadar shugaban kasa ta White House domin fara wa’adinsa na biyu akan karagar mulki.

Mutane wajen dubu dari takwas ne ake tsammanin zasu hallara a farfajiyar da ake kira National Mall, dake gaban ginin Majalisar dokokin Amurka. Wannan kiyasi dai ya gaza na bikin rantsar da Obaman a wa’adinsa na farko a inda kusan mutane miliyan biyu ne suka bayanna domin gani an rantsar da shugaban kasa na farko mai launin bakar fata.

A hukumance, Mr. Obama ya riga ya dauki rantsuwar kama bakin aiki jiya lahadi saboda kundun tsarin mulkin Amurka ya sharrada da’a ranstar da shugaban kasa ran 20 ga watan junairu. Babban alkali mai shari’a John Roberts ne ya jagoranci rantsarwar, kamar yadda yayi wa shugaban a shekara ta 2009.

Bikin rantsar da shugaban kasa na yau ya zone rana daya da ran tunawa da haihuwar Mr. King.
XS
SM
MD
LG