Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa Na Barazanar Daukan Mataki Akan Koriya Ta Kudu


Motar yakin Koriya ta Arewa kennan.
Motar yakin Koriya ta Arewa kennan.
Koriya ta Arewa ta yi barazanar daukar matakan mayar da murtani akan Koriya ta Kudu in har Koriya ta Kudun ta shiga cikin layin rukunin kasashen dake kokarin aiwatarda tsauraran takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sakawa wa Koriya ta Arewa.

A wani bayani da aka fidda yau jumma’ daga kwamitin da arewacin kasar ta kafa akan tabbatarda zaman lafiya tsakanin arewa da kudancin kasar, kwamitin ya yi kashedin cewa sa takunkumi tamkar yin yakine da Koriya ta Arewa.

Sanarwar kuma ta yi barazanar kawo karshen duk wata tattaunawa akan dena yin makaman nikiliya.

Rana larabar da ta wuce, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harba rokar da Koriya ta Arewa ta yi a watan disambar da ta gabata, ta bayyana wannan a matsayin saba wa takunkumin da ya hana yin makami mai lizami da kuma na’urar nukiliya.

Kan hakan ne, Koriya ta Arewa ta maido da murtani a jiya cewa zata yi gwajin makaman nukiliya zata kuma kara harba wasu rokokin.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG