Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeria Tayi Allah Wadai da Barazanar 'Yan Tsageran Niger Delta


Hoton wasu daga cikin 'yan tsageran Movement for the Emancipation for the Niger Delta, (MEND) da aka dauka Febwairu. 24, 2006 file photo.
Hoton wasu daga cikin 'yan tsageran Movement for the Emancipation for the Niger Delta, (MEND) da aka dauka Febwairu. 24, 2006 file photo.
WASHINGTON, D.C -- Gwamnatin Najeria tayi Allah wadai da wata sabuwar barazana da kungiyar ‘yan tsageran nan ta yankin Niger Delta ko Movement for the Emancipation of Niger Delta wato MEND a takaice, tayi mata a baya-bayannan.

Wannan kungiya dai ta dauki alhakin kai hare-hare akan kamfanonin mai, fashe-fashen bom, da satar mutane domin garkuwa da su tun shekara ta 2006.

Wakiliyar Muryar Amurka daga Abuja Heather Murdock tace a cikin barazanar da kungiyar tayi a karshen makon da ya wuce, MEND tace tana shirin kaiwa jami’an Najeria hari, da kamfanonin Afirka ta Kudu, da ma’ajiyar man fetur, da kamfanonin tatar mai a Najeria har ma da ketare domin nuna fushinsu dangane da samun shugabansu da aka yi da laifi, Henry Okah, a Afirka ta Kudu.

A makon da ya wuce ne, aka samu Okah da lafuffuka guda 13 da suke alaqa da wani fashewar bom a cikin mota, ta shekara ta 2010, har mutane 12 suka mutu a babban birnin Najeria Abuja.

Jiya lahadi, Ministan yada labaran Najeria, Labaran Maku yayi Allah wadai da barazanar wannan kungiya, kuma ya kira barazanar a matsayin kalaman marasa kishin kasa.

Minista Mako yace abinda gwamnati take tsammani daga ‘yan Najeria shine nuna karin kishin kasa, da kuma sadaukarwa ga Najeria. Yace Najeria baza ta iya zama kasar da ba’a bin doka ba.

Ana zargin Okah da shugabancin kungiyar MEND din, amma ya musanta hakan. A shekara ta 2010, ya kira kanshi a matsayin mai jimami a wata wayar tarho da yayi da kafar Al-Jazeera daga gidan yari a garin Johannesburg bayan da Najeria ta sa aka kama shi.
XS
SM
MD
LG