Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Shugaban Kasar Paraguay Ya Mutu


Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Lino Cesar Oviedo su na kuka a kofar inda aka kai gawarsa, Lahadi 3 Fabrairu 2013.
Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Lino Cesar Oviedo su na kuka a kofar inda aka kai gawarsa, Lahadi 3 Fabrairu 2013.

Lino Oviedo da ake cacar baki kan tsayawarsa takara ya mutu bayanda jirgin helkwafta da yake ciki ya fadi, amma magoya bayansa su na shakkar yadda abin ya faru.

Wani dan takarar kujerar shugaban kasa da ake cacar baki a kan tsayawarsa takara a kasar Paraguay, ya mutu a faduwar wani jirgin saman helkwafta.

Hukumomi sun ce Lino Cesar Oviedo, da wasu mutane biyu sun mutu a lokacin da jirgin saman helkwafta da suke ciki ya fadi cikin hadarin ruwan sama a yankin arewacin Paraguay a ranar asabar. Amma duk da rahoton cewa akwai gagarumin hadarin ruwan sama a lokacin, wasu daga cikin magoya bayan Oviedo sun ce su na tababar yadda jirgin ya fadi.

Oviedo tsohon kwamandan rundunar sojojin kasar Paraguay ne, kuma ya shiga cikin juyin mulkin shekarar 1989 a lokacin da aka hambarar da dadaddiyar gwamnatin kama karya ta shugaba Alfredo Stroessner.

Ya gudu daga kasar Paraguay a shekarar 1996, a bayan da gwamnati ta zarge shi da kulla makarkashiyar yin wani juyin mulkin. A shekarar 1999, lokacin yana zaman gudun hijira a waje, an yi zargin cewa shi ne ya kulla kashe mataimakin shugaban kasar Paraguay na lokacin, Luis Maria Argana, da aka yi.

Daga bisani, Oviedo ya koma kasar Paraguay, inda aka jefa shi a kurkuku a saboda makarkashiyar juyin mulkin 1996, amma kuma kotu ta wanke shi daga sauran laifuffukan da aka tuhume shi da aikatawa.

Al'ummar kasar Paraguay zasu zabi sabon shugaban kasa a watan Yuni. A watan Yunin bara, majalisar dattijan kasar Paraguay ta tsige shugaba Fernando Lugo daga kan kujerar shugabancin kasar, a bayan da ya umurci 'yan sanda da su kori manoma talakawa da suka mamaye wasu manyan gonaki. An kashe manoma 11 da 'yan sanda 6 a wannan yamutsin. Manoman sun yi ikirarin cewa filayen da suka mamaye an yi musu kwacensu ne ta hanyoyin da suka saba ma doka.
XS
SM
MD
LG