Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Goodluck Zai Je Kallon Wasan Kwallon Kafa Na Najeria


Vincent Enyeama AFCON 2013 (AP Photo/Armando Franca)
Vincent Enyeama AFCON 2013 (AP Photo/Armando Franca)
WASHINGTON, DC - Shugaba Goodluck Jonathan na Najeria yace zai je kallon wasan kwallon kafan Najeria idan tayi nasara akan Mali, zuwa wasan karshe a gasar kofin kwallon kafan nahiyar Afirka da akeyi yanzu a Afirka ta Kudu.

A tattaunawar da Aliyu Mustaphan Sokoto yayi da Dr. Muhammad Sunusi, darektan shirya gasa na hukumar kwallon kafan Najeria, Dr. Sunusi ya tabbatar da rade-radin niyar shugaban ta zuwa Afirka ta Kudu domin kallon wasan, idan har Najeria tayi nasara akan Mali a wasan kusa da karshe, wato semi-final da za'a doka ran Larabannan. Dr. Sunusi ya kara da cewa wasu Gwamnoni ma na da niyyar hallartan wannan wasa idan kungiyar Super Eagles din ta samu nasarar zuwa wasan karshe.

Shugaba Goodluck Jonathan da wasu shuwagabannin Najeria kamar Gwamnoni na shan suka daga wajen mutane dangane da yadda ba wuya sun fice daga kasar zuwa kasashen waje, a lokacin da rashin tsaro da matsalolin al-umma masu yawa ke kalubalantar mabiyansu.

Kungiyar kwallon kafan Najeria dai, ta samu nasara akan kungiyar kwallon kafar kasar Ivory Coast ran Lahadin da ta gabata, da ci biyu da daya. Mutane da yawa sunyi tsammanin Ivory Coast din ne zata yi nasara akan Najeria.

Kwallon kafa a Najeria ya kasance tsin-tsiyar dake daure 'yan kasar baki daya. A duk lokacin da Najeria tayi nasara, mutane suna girke bam-bamce bam-bamcensu a gefe daya domin nuna farin cikinsu a matsayinsu na 'yan Najeria baki daya. Misalin wannan nasara itace ta gasar wasannin motsa jiki a turance Olympics, da akayi a shekara ta 1996, fagen da Najeria ta doke goggagun kasashe masu tarin fitattun 'yan kwallon kafa kamar Brazil da Argentina.

Sai dai Dr. Sunusi ya gayawa Muryar Amurka cewa Najeria baza tayi wa Mali kallon kanwar lasa ba. Kamar yadda sukayi a wasannin baya, kungiyar Super Eagles din zata fito domin buga wasan iya kokarinta.
XS
SM
MD
LG