Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kano Ta Hana Bara Da Yawon Talla


Mutane da babura a birnin Kano, dake arewacin Najeria.
Mutane da babura a birnin Kano, dake arewacin Najeria.
WASHINGTON, D.C -- Gwamnatin jihar Kano ta hana yawon talla da bara a birnin Kano, daga ran Litinin 11 ga wannan wata.

Wakilin Muryar Amurka daga jihar Kano, Muhammad Salisu Rabiu ya bayanna wannan sabuwar doka makonni biyu bayan hana daukar mutane akan babura da gwamnatin tayi.

Rahoton Muhammad Salisu yace gwamnatin tayi hakan ne da nufin tsaftace gari, hana 'yan mata yawon banza, da hana zubar da mutunci da bara ke janyowa.

Ya kara da cewa wannan doka zai takali matsalar rashin zuwa makaranta da yara masu talla da bara ke fuskanta. Sannan duk wanda aka kama da karya wannan doka, zai biya tarar naira dubu biyar.

Birnin Kano dai na daya daga cikin birne a yammacin Afirka dake da tarin jama'a, kuma itace cibiyar hada-hadar kasuwanci a arewacin Najeria. Rashin kayan more rayuwa da ayyukanyi yasa mutane da yawa daga karkara suna kaura zuwa wannan birni domin neman na abinci.

Sufurin mutane akan babur da ake kira achaba, talla, da bara na daga hanyoyin da mutane masu dunbun yawa suke samun kudi, saboda rashin ilimi, ayyukanyi da nakasa. Dayawa daga cikin masu wadannan sana'o'i, ba'a san ransu sukeyi ba, sai don sun samu daman biyan bukatansu da tallafawa iyalansu.

A lokacin da sama da kaso 50 cikin 100 na matasan Najeria ke fama da rashin ayyukanyi, manazarta na shakkar duk wani mataki da zai kara adadin marasa ayyukanyi saboda dalilan tsaro.
XS
SM
MD
LG