Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uhuru Kenyatta Na So A Dakatar Da Shari'a


Mataimakin Firayim Ministan Kenya kennan, Uhuru Kenyatta kennan a cikin taron jama'a a birnin Nairobi. Junairu. 30, 2013.
Mataimakin Firayim Ministan Kenya kennan, Uhuru Kenyatta kennan a cikin taron jama'a a birnin Nairobi. Junairu. 30, 2013.

Dan takarar shugaban kasa na Kenya Uhuru Kenyatta na son a dakatar da shar’ar da ake son yi misu a bisa zargin gallazawa wasu da danne taka musu hakkinsu na ‘yancin bil adama.

Kenyatta daya ne daga cikin mutane hudun da ake zargi da kitsa makircin da ya janyo mummunan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da aka yi a can Kenya a 2007.

A da an shirya cewa za’a soma mishi wannan shara’a a Kotun laifukka ta Duniya dake Hague a ran 11 ga watan Afrilun nan mai zuwa, makkoni biyar bayan an gama zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin Kenya din.

Izuwa yanzu dai ba’a ji wani murtani daga su alkallan dake sauraren shara’ar ba, balle kuma ita kotun ta duniya.

A wajen shimfidar shara’ar da aka soma yau Alhamis a can hauge, lauyoyin Kenyatta din sunce lauyoyin dake gabatar da karar sun fito da wasu sababbin magangannu da sheda da ya ssa su ma nashi lauyoyin zasu bukaci karin lokaci don su nazarce su.

Shi dai Kenyatta, wanda tsohon ministan kudi ne a Kenya, ana mishi daukar daya daga cikin ‘yan takara biyu dake sahun gaba a wannan takarar ta shugaban kasa da ake a Kenya. Na biyun shine tsohon frayim-ministan kasar Raila Odinga.
XS
SM
MD
LG