Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar China Zata Saka Kafar Wando Daya da Cin Hanci Da Rashawa


Taron shuwagabannin Chana.
Taron shuwagabannin Chana.

Gwamnatin kasar China tayi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa, da inganta yanayin kasa da kuma bunkasa tattalin arzikinta yayinda majalisar dokokin kasar take fara zamanta na shekara shekara yau Talata.

Dubban wakilai dake fadin kasar sun taru a birnin Beijing karkashin cikakken tsaro domin taron kwana goma sha uku na National People’s Congress da zai zama cikamakin sauyin mulkin kasar da ake yi bayan shekaru goma.

Firai minista mai barin gado Wen Jiabao ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnatinsa na karshe a wajen bude taron. Yace akwai aiki tukuru a gaban kasar China na gyara rashin habakar tattalin arzikinta da kuma gagarumar rata dake akwai tsakanin attajirai da talakawa.

Mr. Wen yace burin kasar China bana kamar na shekarar da ta gabata shine bunkasa tattalin arzikin kasar da kashi bakwai da rabi bisa dari, yayinda gwamnati zata kuma yi kokari ta rage hauhawar farashin kaya. Za a kuma kara yawan kudin da ake kashewa kan harkokin tsaro da kimanin kashi goma sha daya bisa dari,

A lokacin taron majalisar dokokin da bata da tasiri, shugaban jam’iyar Kwaminis na kasar China, Xi Jinping zai karbi ragamar shugabanci daga shugaba Hu Jintao. Li Kenqiang zai gaji Mr. Wen a matsayin Firai Minista.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG