Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Shirye Muke Mu Hukunta Koriya Ta Arewa - inji Koriya Ta Kudu


Tutar Koriya ta Arewa
Tutar Koriya ta Arewa

Ma’aikatar tsaron koriya ta kudu tayi alwashin daukatar mataki mai karfi idan har koriya ta arewa ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi dake tsakaninsu na tsawon shekaru 60.

Janar Kim Yong-hyun yau laraba yace Koriya ta Kudu a shirye take ta kai hari ga inda wannan barazana ta samo asali, da kuma inda ake bada umarni na wannan barazana idan dai har Koriya ta arewan tayi amfani da karfin soji.

A jiya Talata, wani babban kwamandan koriya ta Arewa yace kasarshi zatayi kafar ungulu da yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi da suka rattabawa hannu a shekara ta 1953, wanda shine ya kai karshen yakin Koriya, kuma kwamandan ya ambacin takunkumi da Amurka ta jagoranta aka kakaba musu, da kuma atisayen Soji da Amurka da Koriya ta Kudu sukeyi a matsayin dalilan yin watsi da wannan yarjejeniya.

Sai dai kuma ba abin mamaki bane a ji irin wadannan kalamai daga koriya ta Arewa, balle ma a lokacin da ake zaman dar-dar. Manazarta sunce wannan barazana zata iya zuwa da muhimmanci saboda babban hafsin soji ne yayi ta, kuma ya bada wa’adi.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG