Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Damu Da Iran


Wata ma'aikatar sarrafa Nukiliyar Iran.
Wata ma'aikatar sarrafa Nukiliyar Iran.

Kasar Amurka ta nuna damuwarta akan yadda kasar Iran take kin amsa tambaboyi dangane da harkokinta na nukiliya, tana mai cewa Tehran na amfani ne da yaudara, toshe kunnuwa da bata lokaci.

Da yake ganawa a garin Vienna yau laraba, Joseph Macmanus, shugaban wakilan Amurka a hukumar harkokin nukiliya ta kasa da kasa yace Iran ta cigaba da takalar rigima a maimakon yin abinda ya kamata tayi.

Yace baza a amince da yunkurin Iran ba na neman makaman Nukiliya, kuma abinda kasar keyi zai sa ta zama saniyar ware daga kasashen duniya.

Iran dai tace ita sam, bata kera makaman Nukiliya. Tace harkokinta na zaman lafiya ne kawai.

Shugaban hukumar harkokin nukiliya ta duniya Yukiya Amano ran litinin yace idan iran bata cigaba da bada hadin kai ba, masu bincike baza su iya tabbatarwa harkokin iran na zaman lafiya ne ba. Yace dole ne a cigaba da sulhu da Iran a cikin gaggawa.
XS
SM
MD
LG