Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NASA Ta Ce, Mai Yiwuwa Ne An Rayu A Duniyar Mars


Na'urar Curiosity dauke da garin da ta hako daga cikin wani dutse a duniyar Mars
Na'urar Curiosity dauke da garin da ta hako daga cikin wani dutse a duniyar Mars

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA, ta ce na’urar ta, ta Curiosity ta samo wata shaida mai nuna cewa an yi rayuwa a duniyar Mars.

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA, ta ce na’urar ta, ta leke-leke a duniyar Mars ta tattara shaida ta hakika wadda ke nuna cewa a wani zamani an taba samun wata halittar da ta rayu a duniyar ta Mars.

Masana ilimin kimiyyar hukumar NASA, sun yi cikakken nazari da bincike a kan wani gari da na’urar Curiosity ta hako daga cikin wani dutsi a watan jiya. Sun ce dutsen ya kunshi wasu ma’adinan tabo ko yumbu, irin wadanda ake samu a yanayin da ke da ruwa. Haka kuma sun gano wasu ababe da dole sai da su ake iya rayuwa, kamar iskar Hydrogen, da iskar shaka ta Oxygen da kuma sinadarin Nitrogen.

Masanin ilimin kimiyya, John Grotzinger ya ce ruwan da ya taba kwanciya a duniyar Mars, ruwa mai lafiya wanda ake iya sha.

Ba a sawa na’urar Curiosity kayan gano mitsi-mitsin halittun da ido ba ya iya gani, wadanda ke raye yanzu haka a duniyar ta Mars ko kuma matattun mitsi-mitsin halittun da suka rayu a duniya tun shekaru aru-aru da suka wuce wadanda yanzu babu su.

Masana ilimin kimiyya sun yi amanna cewa, a zamanin da can, duniyar Mars wuri ne mai dumi da damshi kafin ya zama kekashasshen hamada mai tsananin sanyi.
XS
SM
MD
LG