Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Yunkurin Cimma Matsaya Akan Harkokin Cinikayyar Makamai


Shuwagabannin duniya a taron yarjejeniyar cinikin makamai.
Shuwagabannin duniya a taron yarjejeniyar cinikin makamai.

An koma teburin tattaunawa cikin makon nan da nufin cimma matsaya kan abinda ya yiwu ya zama wata ci gaba a yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ta sa ido kan harkokin cinikayya makamai ta duniya da ake kashe biliyoyin dala akai.

An fara tattaunawar ne yau Litinin a shelkwatar Majalisar Dinkin Duniya. An tashi a tattunawar da aka yi ta tsawon makonni a watan Yuli ba tare da cimma matsaya ba, sakamakon bukatar da Amurka da Rasha da kuma China suka gabatar suna neman karin lokaci.

Masu goyon bayan sa ido kan yadda ake amfani da makamai sun ce ana bukatar yarjejeniyar domin a hana safarar miyagun makamai zuwa kasashen da dake tashin hankali abinda zai ruruta wutar yaki da kuma aikata miyagun laifuka.

Amurka, kasar da tafi kowacce a duniya kera makamai, ta jadada ranar jumma’a cewa, tana adawa da duk wani shirin da ya kunshi harsashi sabili da tsada da kuma wahalarwa wajen sa ido a kai.

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya yi kira da a sa albarusai a cikin yarjejeniya.

Washington tana adawa da duk wani abinda ya sabawa kundin tsarin mulkin Amurka da ya bada ‘yancin mallakar makamai.
XS
SM
MD
LG