Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uhuru Kenyatta Na So A Janye Zargin Aikata Laifukan Cin Zarafin Bil'adama Da Ake Yi Masa


Shugaban Kenya mai jiran gado, Uhuru Kenyatta.
Shugaban Kenya mai jiran gado, Uhuru Kenyatta.

Lauyoyin shugaban kasar Kenya mai jiran gado Uhuru Kenyatta sun yi kira ga kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa da ta janye zargin aikata laifukan cin zarafin bil’adama da take yi masa.

Alkalai a kotun dake zama a birnin Hague sun shaidawa wani zaman da aka yi yau litinin domin nazarin ko za a yi watsi da zarge zargen bayan da aka yi fatali da karar da aka shigar kan Francis Muthaura mutum na biyu da ake zarginsu da aikata laifukan.

Lauyoyin dake kare shi sun ce kotun tana dogara ne ga shaidar wani mutum da ya janye shaidar da ya bayar da farko.

Mr. Kenyatta da Muthaura suna cikin ‘yan kasar Kenya hudu da ake zargi da kitsa tashin hankalin da aka yi asarar rayuka a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta dubu biyu da bakwai.

Ana zarginsu duka biyu da laifin aikata laifin gallazawa bil’adama da ya hada da kisan kai, da tilasa al’umma kaura da kuma fyade. Sun musanta aikata laifukan.
XS
SM
MD
LG