Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Henry Okah Ya Samu Hukuncin Shekaru 24 A Kurkuku


Dan Najeriya wanda aka samu laifin ta'adanci Henry Okah, a kotun Afirka ta Kudu. Junairu 21, 2013.
Dan Najeriya wanda aka samu laifin ta'adanci Henry Okah, a kotun Afirka ta Kudu. Junairu 21, 2013.

Wata kotun Afrika ta Kudu ta yanke wa wani rikakken dan tada zaune tsaye na Nigeria Henry Okah hukuncin daurin shekaru 24 bayanda ta same shi da laifin yin hannu a dfarmakin ta’addacin da aka kai a Abuja, babban birnin tarayyar Nigeria a lokacinda ake shagulgullan samun ‘yancin kai na shekarar 2010.

WASHINGTON, D.C - Kotun ta kuma kama shi da laifin kitsa makiricin yi wa gwamnatin Afrika ta Kudu barazana. Ana zargin Okah da laifin yin jagorancin kungiyar ‘yan tsageran yankin Niger delta ta MEND, wacce ta dauki alhakin kai wancan harin.

Shi kansa ya musanra cewa yana da hannu a kai harin.

Wannan kungiyar ta MEND ta dade tana kai hare-hare barkattai akan masna’antun man fetur a bisa hujjar cewa tana neman babban kaso na riubar da ake samu daga man fetur din da ake tatsowa daga yankin nasu na Niger Delta.

Sai dai daga baya, da yawa daga cikin ‘yan kungiyar ta MEND, sun ajiye makamansu na fada a karkashi wani shirin ahuwa da aka kulla tsakaninsu da gwamnati.
XS
SM
MD
LG