Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Bama-Bamai Da Makamai A Kano


'Yan sandan Najeriya a Kano, su na baje makamai da bama-bamai da albarusai da suka kwace daga hannun wasu 'yan bindiga Laraba 27 Maris 2013
'Yan sandan Najeriya a Kano, su na baje makamai da bama-bamai da albarusai da suka kwace daga hannun wasu 'yan bindiga Laraba 27 Maris 2013

An yi kwanton bauna, aka far ma 'yan bindigar su hudu cikin wata mota a kauyen Inusawa dake karamar hukumar Ungogo a cikin daren talatar nan

'Yan sanda a Jihar Kano dake arewacin Najeriya, sun far ma wasu 'yan bindiga a kauyen Inusawa dake karamar hukumar Ungogo, inda a bayan da suka shafe tsawon lokaci su na musayar wuta da bindigogi, mutanen suka gudu suka bar makamai da bama-bamansu.

Kwamishinan 'yan sanda a Jihar Kano, Alhaji Musawa A. Daura, shi ya bayyana wannan a lokacin da yake ganawa da 'yan jarida yau laraba a Kano, a bayan da jami'an tsaro suka tattaro bindigogi da bama-bamai da albarusai, da kuma kunamun tayar da su da 'yan bindigar suka tsere suka bari cikin motarsu.

Kwamishinan ya ce "Mun samu rahoto (na sirri) cewa akwai wasu miyagun mutane sun shigo cikin Kano, wadanda aniyarsu ba ta alheri ba ce, domin su (kai hari kan) mutane su kashe, su kuma kwashe kayayyakinsu."
Makamai da Bama-baman da 'yan sanda suka gano yau ;laraba a Kano
Makamai da Bama-baman da 'yan sanda suka gano yau ;laraba a Kano


Alhaji Musawa A. daura ya kara da cewa samun wannan rahoto ke da wuya, sai suka yi harama suka garzaya zuwa inda aka tsegunta musu mutanen suke, kuma daga ganin 'yan sanda sai mutanen suka bude musu wuta, su kuma 'yan sanda suka maida martani.

A bayan musayar wuta ta tsawon lokaci ne sai 'yan bindigar suka tsere cikin daji, kuma kwamishinan yace har yanzu su na bin sawunsu, domin sun raunata wasu daga cikinsu.

Makaman da aka samu cikin motar da 'yan bindigar suka gudu suka bari, sun hada da "bindiga kirar AK-47 guda daya, da wata bindigar kai farmaki guda daya, da harsasai guda 238, da makamin harba roka, da kwanson zuba harsasai guda 8, da bama-bamai hadin gida da aka dana cikin galan na man girki guda 7, da silinda 2 na gas, da gurnetin hannu 14 da aka dasa cikin karamar roba ta madara..." in ji kwamishinan 'yan sandan.

A ranar asabar da ta shige ma, sai da aka samu tashin wasu bama-bamai har guda biyu, wadanda suka kashe mutanen da suka yi niyyar kai hari da su, a hanyar da ta kewaye Kano ta gabas wadda ake kira Bye-Pass.
XS
SM
MD
LG