Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burma Ta Kafa Hukumar Binciko Wutar Da Ta Kona Masallaci


Mutane dauke da makara lokacin jana'izar wadanda suka mutu a gobarar da ta tashi a wata Cibiyar Musulmi a Rangoon, Burma
Mutane dauke da makara lokacin jana'izar wadanda suka mutu a gobarar da ta tashi a wata Cibiyar Musulmi a Rangoon, Burma

Yara kanana 13 suka mutu a wannan gobarar da Musulmi a birnin suka ce da gangan aka cinna ta a wata cibiyar Islamiyya a babban birnin na Burma

Burma ta bayar da sanarwar kaddamar da bincike game da wata gobarar da ta tashi a wata Cibiyar Islamiyya dake birnin Rangoon, har ta kashe yara kanana su 13, a bayan da Musulmi da dama a birnin suka bayyana damuwar cewa da gangan aka cinna wannan wuta.

Jaridar "New Light Myanmar" mallakar gwamnati ta fada yau laraba cewa wata hukumar bincike mai wakilai 7 zata bi sawun wannan gobara wadda jami'an birnin suka ce wata matsalar wutar lantarki ce ta janyo ta.

Wannan gobara ta jiya talata, ta tashi a tsakiyar lokacin da ake ta tashin hankali na nuna kin jinin Musulmi a kasar Burma, inda aka lalata Masallatai da kadarori na Musulmi a birane da dama a yankin tsakiyar kasar.

An ci gaba da daukar matakan tsaro masu yawa yau laraba a kofar wannan Masallaci na Rangoon a yau laraba, inda 'yan sandan kwantar da tarzoma suke ci gaba da yin sintiri a titin da wannan masallaci yake. Hukumomi su na fargabar cewa wannan lamarin yana iya kara rura wutar tashin hankalin addini a wannan kasa inda mafiya yawan al'ummarta masu bin addinin Buddha ne.

Gwamnati ta ce zata bayyana sakamakon wannan bincike a ranar jumma'a.
XS
SM
MD
LG