Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin G8 Na Ganawa a London


Ministocin harkokin waje a taron G8
Ministocin harkokin waje a taron G8

Ministocin harkokin wajen kasashe 8 da suka fi arziki a duniya, G8 a takaice, suna ganawa yau a birnin London.

WASHINGTON, D.C - Manyan batutuwan da suke tattaunawa sun hada da zaman dar-dar a makurdadar Koriya, da rigima da ake yi a Syria, da kuma shirin Nukiliyar kasar Iran.

Koriya ta Arewa ta yi ta aika barazanar yaki zuwa ga Amurka da Koriya ta Kudu a makonnin da suka wace, kuma tace a shirye take tayi gwajin makami mai linzami.

A gefe daya a wajen taron, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwell yace kasashen na G8 sun amince akan cewa barazanar da Koriya ta Arewa take yi bai dace ba.

Jiya laraba, wasu ministocin harkokin wajen sun tattauna da jami’an adawar Syria. Sakataren harkokin wjaen Amurka John Kerry da Sakataren harkokin wajen Britania William Hague sun saurari kira da masu adawar Syria suke yi musu, na neman Karin agajin kayan soji, sai dai wani jami’in Amurka yace ba’a yi musu alkawarin komai ba.
XS
SM
MD
LG