Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Girgizar Kasa A Iran da Pakistan


Mutane suna ficewa daga gidaje a Pakistan.
Mutane suna ficewa daga gidaje a Pakistan.

Wata gagarumar girgizar kasa ta jijjiga yankunan dake kudu-maso-gabashin Iran da makwapciyarta Pakistan, inda izuwa yanzu aka tabatta ta kashe mutane biyar, ta raunata wasu da yawa.

WASHINGTON, D.C - Hukumar auna karfin girgizan kasa ta Amurka ta yi hasashen cewa karfin girgizar zai kai kamar maki 7.8, ta kuma cewa girgizar ta soma ne daga wani wuri dake tsakiyar biranen Khas da Saravan na kasar Iran din.

Sai dai hukumar auna karfin gigizar kasar ta Iran ta rage karfin ta da cewa misali mai maki 7.5 ce, amma ta tabattar da cewa ta afru ne da karfe 3.14 na La’asariya, agogon Iran a yau Talata.

Su ma hukumomin Pakistan sunce tarin gidaje da yawa sun roshe a lardin Balochistan dake kan iyakar Iran da Pakistan. Sun kuma ce an zaro gawawwaki da dama daga cikin gine-ginen da suka rosa din.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG