Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom Ya Fashe A Ofishin Jakadan Faransa Dake Libiya


Mutane sun yi dafifi a wajen ofishin jakadancin Faransa dake Libiya.
Mutane sun yi dafifi a wajen ofishin jakadancin Faransa dake Libiya.

Kasar Faransa tayi Allah wadai da wani fashewar Bom da aka saka a mota, a ofishin jakadancinta dake babban birnin Libya, tana kiran harin a matsayin wani mugun abu.

WASHINGTON, D.C - Jami’ai sunce fashewar ta safiyar yau Talata a ofishin jakadancinta dake unguwar Hay Andalus a birnin Tripoli, ta ji wa masu gadi guda biyu raunuka, kuma tayi barna sosai. Ofishin harkokin wajen Libiya ya kira wannan abu a matsayin “harin ta’addanci”.

Shugaban Faransa Fransuwa Hollande yace gwamnati na sa ran jami’an Libiya zasu taimaka, wajen gano dalilin kai wannan hari, da kuma gurfanar da wadanda suka aikata hakan a gaban kuliya.

Ya kara da cewa ana kai harin bom ne ga duka kasarshen dake da hannu wajen yakar ta’addanci.

Kasar Libya dai na fama da tashe-tashen hankula da rashin kwanciyar hankali tun bayan da aka tunbuke shugabanta mai mulkin kama karya, kuma wanda ya dade akan karagar mulki Moamar Gadhafi a karshen shekata ta 2011.

Wani hari akan ofishin jakadancin Amurka dake Benghazi a watan Satumbar da ta wuce ya kashe jakadan Amurka da wasu Amurkawa guda 3.
XS
SM
MD
LG