Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe 'Yan Boko Haram Da Dama Jiya Lahadi


Dakarun Najeriya su na sintiri a garin Bama
Dakarun Najeriya su na sintiri a garin Bama

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe mayakan Boko Haram 14, suka damke wasu guda 20 jiya lahadi, yayin da ake ci gaba da fafatawa a yankin arewa maso gabas.

Rundunar sojojin Nanjeriya ta ce ta kashe mayakan Boko Haram goma sha hudu ta kuma cafke wasu guda ashirin Lahadin nan, yayin da dakarun ke cigaba da matsawa kungiyar a arewa maso gabashin kasar wadda kuma ke da alaka da kungiyar al-Qaida.

Mai magana da yawun rundunar, Janaral Chris Olukolade, yace an kashe sojoji uku a cikin gumurzun. Rikicin ya kara tsamari makon da ya wuce a sanadin abinda rundunar ta bayyana a zaman farmaki mafi girma da ta taba kaddamarwa a kan 'yan bindigar tun lokacin da suka fara tayar da kayar baya a shekarar 2009.

Mai magana da yawun rundunar bai bayyana inda fadan ya auku ba amma yace dakarun gwamnati na fafatawa cikin kwanaki biyun da suka gabata da mayakan Islama wadanda suka mallaki mugayen makamai.

Boko Haram, wadda ta ke kokarin kafa daular Islama a arewacin Najeriya, ta kai hare-haren bama-bamai da harbe-harbe a arewa, ciki har da munanan hare-hare a kan wasu garuruwa biyu cikin makonni takwas da suka gabata. Jami’ai sun ce mutane dari biyu da hamsin aka kashe a hare-haren da a ka kai kan garuruwan Baga da Bama.

A halin da ake ciki, an rufe bakin iyakar Najeriya da Kamaru, bayan da kasashen biyu suka cimma daidaito kan yadda za a tabbatar da nasarar matakan da aka dauka na damke 'yan bindigar da zasu yi kokarin sulalewa.

Wakilin sashen Hausa, Ibrahim Abdulaziz, ya aiko da karin bayani kan wannan daga Yola, hedkwatar Jihar Adamawa.

Rahoton Ibrahim Abdulaziz Daga Yola Kan Rufe Bakin Iyakar Najeriya Da Kamaru - 2:24
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG