Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Akalla 21 A Maiduguri


Sojojin Najeriya a kauyen Hausari, kusa da Maiduguri, 5 Yuni 2013, a yayin da suke ci gaba da farautar 'yan Boko Haram
Sojojin Najeriya a kauyen Hausari, kusa da Maiduguri, 5 Yuni 2013, a yayin da suke ci gaba da farautar 'yan Boko Haram

Shaidu sun ce an kashe mutane akalla 21 cikin kwanaki biyun da suka shige a Maiduguri a fada da 'yan Boko Haram

Shaidu a Najeriya sun ce an kashe mutane akalla 21 a birnin Maiduguri, dake arewa maso gabashin kasar, cikin kwanaki biyun da suka shige, a yayin da nsojojin gwamnati ke ci gaba da kai farmaki a kan n'yan Boko Haram.

Gwamnati ta ce an kashe 'yan Boko Haram su akalla 8 ranar alhamis a birnin na Maiduguri. A ranar jumma'a kuma, an yi kashe-kashen da aka bayyana a zaman alamun na daukar fansa ne da aka kai a kan wasu 'yan banga wadanhda suka taimakawa gwamnati wajen zakulo 'yan Boko Haram.

Kafofin labarai na Najeriya da na kasashen yammaci sun ce 'yan Boko Haram sun yi sumogar makaman da suka yi amfani da su wajen kai hare-haren ranar jumma'a, suka wuce da su ta wuraren da jami'an tsaro suke bincike, a bayan da suka boye su a cikin wata makarar daukar gawa.

An kasa samun hanya mai zaman kanta ta tabbatar da sahihancin rahotannin na gwamnati ko na 'yan Boko haram a saboda rashin layukan tarho da kuma hana zuwa bakin dagar a arewa.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kama 'yan Boko Haram su fiye da 150 tun lokacin da ta kaddamar da wannan farmaki a watan da ya shige.
XS
SM
MD
LG