Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya zata biya wadanda rikicin zaben 2011 ya rutsa da su diyya


Wani da rikicin da ya biyo bayan zaben 2011 ya shafa
Wani da rikicin da ya biyo bayan zaben 2011 ya shafa
Gwamnatin Najeriya zata biya wadanda rikicin zaben 2011 ya rutsa da su diyya. A karo na farko ta fitar da nera miliyan dubu goma sha biyar na biyan jihohi tara. Cikin jihohin har da ma jihar Bauchi inda wakilinmu ya samu ya zanta da wasu da abun ya shafa.

A cikin kudin da aka ware ma jihohi tara a kashin farko, jihar Bauchi zata samu nera miliyan dubu daya da miliyan dari bakwai. To sai dai babu wanda kason suka shigo hannunsa tukunna a jihar Bauchi. Wani Alhaji Auwalu Karfen Ningi ya ce shi da sauran mutane talatin da hudu da suka yi asarar dukiyoyinsu ko kwabo basu samu ba tukunna. Sun tattaka zuwa ofisoshin karamar hukuma da na jiha basu ci nasara ba. A jihar jami'an gwamnati sun ce su ma a kafar radiyo suka ji amma babu abun da ya shigo aljihun gwamnatin jihar game da biyan diyar.

Wakilinmu Abdulwahab Mohammed ya yi karin bayani a rahotonsa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG