Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Ma Kwamitin Sulhu Da Boko Haram Wa’adi


Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan yace Kwamitin yana cimma tazara, kuma har yanzu yana son a warware rikicin ta hanyar lumana.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yace har yanzu yana son ganin an warware rikicin Boko Haram ta hanyar lumana, kamar yadda kwamitin da ya kafa kan yin sulhu da ahuwa yake kokarin yi.

An shirya kwamitin zai gabatar da rahotonsa ga gwamnati a cikin wannan makon, amma a jiya talata, shugaban na Najeriya ya kara ma wannan kwamiti watanni biyu domin ya ci gaba da kokarin da yake yin a neman hanyoyin kawo sulhu.

Shugaba Jonathan yace kwamitin yana samun ci gaba a wannan aiki da yake yi, duk da furucin da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya sha yi a cikin hogtunan bidiyon da suke sanyawa kan intanet cewa sub a zasu tattauna sulhu da gwamnatin ba.

Shugaban Kwamitin, Barrister Tanimu Turaki, wanda shi ne ministan ayyuka na musamman a gwamnatin shugaba Jonathan, ya fadawa ‘yan jarida cewa, “muna tattaunawa mai matukar muhimmanci da ‘yan tawaye…tattaunawar da ba wai kawai zata kai ga kulla yarjejeniyoyin tsagaita wuta ba ne, zata ma kai mu ga ajiye makamai baki daya.”
XS
SM
MD
LG