Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Giwaye Ta Duniya 12 Agusta


Yau take ranar 12 ga watan Agusta, ranar da aka ware musamman domin janyo hankalin duniya ga halin da giwaye suke ciki a fadin duniya, musamman a nahiyar Afirka, gidansu na asali.

Beatrice Karanja, ta Gidauniyar Namun Daji A Afirka ta ce makasudin Ranar Giwaye ta Duniya shi ne jaddada kokarin ceton wannan naman dajin da babu kamarsa, wanda ake kashewa gadan-gadan a nahiyar Afirka domin kawai a cire haurensa.

Ta ce a shekarar da ta shige, Afirka ta yi hasarar giwaye dubu 35, kuma idan wannan abu ya ci gaba da tafiya haka ba a yi komai a kai ba, to nan da shekarar 2025, ko shekaru 11 masu zuwa, dukkan giwayen dake daji a Afirka zasu kare.

Maharban dake satar kashe giwaye a yanzu su na amfani da na'urorin zamani kamar tabaron gani cikin duhu, makamai masu karfi na zamani da na'urorin GPS masu amfani da tauraron dan Adama wajen nuna zahirin inda giwayen suke da wasunsu.

A wani gefen, kokarin da ake yi na ceton giwaye yana aiki. Alal ga misali, sintiri a kafa da kuma jiragen sama da ake yi a gandun namun daji na Lower Zambezi National Park a kasar Zambiya, ya rage yawan kashe giwaye da kashi 50 cikin 100. Akwai giwaye kimanin dubu 2 da dari biyu a wannan gandu.

XS
SM
MD
LG