Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gangamin Kan Ilmin Diya Mata A Fadin Duniya.


Shugaban Amurka da shugaban China da uwargidajensu a fadar White House.
Shugaban Amurka da shugaban China da uwargidajensu a fadar White House.

Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama ce ta kaddamar da shirin jiya a New York.

Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama ta kaddamar wani shiri jiya Asabar a wani biki na kara jawo hankali kan rashin sanya 'yaya mata a makarantu, da kuma gibi dake akwai a rayuwar jama'a a fadin duniya.

Wannan sabon shiri mai lakabi 'yan mata milyan 62, an shirya shine da zummar jawo hankalin duniya cewa miliyoyin 'yan mata a fadin duniya basa zuwa makaranta.

Mrs Obama tace hakikance kan baiwar da Allah Ya yiwa 'yan mata a fadin duniya bata da iyaka", a bikin da aka dandalin shakatawa da ake kira Central park dake birnin New York. Madam Michelle ta ci gaba da cewa "yanzu haka 'yan mata milyan 62 basa zuwa makaranta, suna 'yancin samun ilmi, kamar 'yayanmu mata, kamar 'yaya na. Basu wannan dama inji uwargidan shugaban na Amurka yana da muhimmanci wajen kawo karshen talauci a duniya.

Cikin wadand suka yi jawabi a bikin, harda matashiyan nan 'yar kasar Pakistan da ta sami lambar yabo ta Nobel, Malala Youssefzai, mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, mawakiyar nan Beyonce, dan wasan kwaikwayo a fina-finan Amurka Leonardo Decaprio, Sarauniya Rania na Jordan, suna daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a bikin.

Shugaban Amurka Barack Obama yayi magana ga mahalarta bikin ta vidiyo daga Fadar White House.

XS
SM
MD
LG