Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Ministan Tsaron China Dauri Shekaru 12 A Gida Yari


Ministan Tsaron China
Ministan Tsaron China

Ministan na daya daga cikin masu mukami mafi girma da aka taba samu da laifin cin hanci

An yanke hukuncin daurin shekaru goma sha biyu a gidan yari ga mai taimakawa tsohon ministan tsaron kasar China domin samun sa da laifin karban cin hanci.

Kanfanin dillacin labarai na kasar China Xinhua yace an samu Ji Wenlin wanda ya taba zama tsohon mukaddashin gwamnan kudancin gundumar Hainan da laifin karban cin hancin dala miliyan uku.

A wannan lokacin Ji Wenlin yana aiki ne da tsohon ministan Zhou Yongkang a gwamnatin kasar. Zhou wanda tsohon dan jamiyyar kwaminisanci ne yana daya daga cikin masu mukami mafi girma da aka taba samu da irin wannan laifin na cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaba XiJinping keyi

Yanzu haka dai an daure Zhou na tsawon rai-da-rai gidan yari domin karban cin hanci, da anfani da muklamin sa fiye da kima da kuma bude sirrin gwamnati.

XS
SM
MD
LG