Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa Francois Hollande Ya Jingine Shirin Canji Kundin Tsarin Mulkin Kasar


Francois Hollande
Francois Hollande

Batun ya fuskanci turjiya daga masu hasashen cewa wannan na iya zamowa kamar bita da kulli ne ga Musulmai.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya fada yau laraba cewa ya jingine shirin sa na neman canji a kundin tsarin mulkin kasar wanda ya hada da matakin kwace ‘yancin zama dan kasa ga haifaffun kasar Faransa, wadanda aka samu da yin taaddanci.

Shugaba Francois ya kuduri hakan ne bayan harin ta’addanci da aka kai kasar cikin watan Nuwamban bara aka halaka mutane 130 kana aka jima sama da 350 rauni, sai dai Majilisar dattijai data wakilan kasar sun kasa cimma matsaya kan dokar.

Hollande yace nufin sa shine ya kara kawo hadin kai cikin kasar tare da nuna cewa zata iya mayar da martini a duk lokacin da ta'addanci ya kunno kai.

Wannan kudirin ya fuskanci turjiya daga masu hasashen cewa wannan na iya zamowa kamar bita da kulli ne ga Musulmai.

Wasu daga cikin su sun kwatanta wannan da karbe halarcin zama dan kasa da akayi wa Yahudawa lokacin yakin duniya na biyu.

Wannan yunkurin ne dai yasa Ministan sharaa na kasar ya sauka daga kan mukamin sa saboda bai yarda da shirin na shugaba Hollande ba.

Shugaban yace duk da yake ya jingine wannan yunkurin na gyarar kundin mulkin kasar, amma har yanzu yana nan kan bakar sa natabbatar da tsaro da kare ‘yan kasar daga ‘yan taadda.

XS
SM
MD
LG