Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Mutane 11 Da Aikata Kisa


A kwashe watanni 3 ana tashin hankali wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 1000 shekaru 14 da su ka gabata

Wata kotun Indiya ta zartas da hukunci kan wasu mutane 26 a yau dinnan Alhamis, saboda rawar da su ka taka a kisan wasu Musulmi 69 da mabiya addinin Hindu su ka yi a jahar Gujarat a 2002.

An tuhumu 11 daga mutane 24 da aikata kisa a daya daga cikin al'amari mafi muni a tashin hankalin da aka kwashe watanni 3 ana yi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 1000 shekaru 14 da su ka gabata.

Daya daga cikin mutune 69 din da au aka make shi, au aka kona shi har lahira yayin da ya fake a wani rukunin gidaje a Ahmedabad, wani tsohon Dan Majalisar Dokoki ne mai suna Ehsan Jafri.

Matar marigayi Jafri, Zakia ta yi farinciki da wannan hukuncin, to amma ba ta ji dadin sallar wasu mutane 36 da ake zargi da alkalin ya yi ba.

"Wannan ba cikakken adalci ba ne don haka zan cigaba da fafatuka har makura," a cewarta ga manema labarai.

Tun daga 2002 an zartas da hukunci kan mutane 100 game da wannan tashin hankalin, to amma har yanzu akwai wasu shari'un da ba a fara saurare ba.

XS
SM
MD
LG