Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bin Sabuwar Hanya Domin Farfado Da Kasar Somaliya


Dole ne Amurka ta bi wata hanya ta daban a kokarin da take na taimakawa farfado da kasar Samaliya,

Dole ne Amurka ta bi wata hanya ta daban a kokarin da take na taimakawa farfado da kasar Samaliya, biyo bayan nada jakadan Amurka na farko a Somaliya sama da shekaru 25 da suka gabata, a cewar tsohon ma’aikacin diflomasiya kuma mai fashin baki kan harkokin kasashe.

Abub'kar Arman, tsohon wakilin Somaliya na musamman Amurka, ya fada a jiya Laraba cewa Amurka na da rauni wajen rashin yin amfani da karfinta a kokarin da take na taimakawa gwamnatin Somaliya wajen dawo da tsaro da ci gaban harkar siyasa.

Arman yace nada Stephen Schwartz a matsayin jakada a Somaliya wani babi ne na tarihi, amma yace dole ne sabon jakadan yayi amfani da damarsa don ganin an sake bude asusun cire kudade a Amurka.

Damuwar bankuna kan wannan kudi dai shine kar ya fada hannun mutanen da bai kamata ba. amma yanzu kudaden basa cikin bankuna.

XS
SM
MD
LG