Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Tarurrukan Yaki Da Cutar Kanjamau


Sashen Hausa na Muryar Amurka ya kaddamar da tarurrukan koli na yaki da cutar kanjamau a garuruwa uku a Nijeriya.

Makasudin wadannan tarurruka shi ne wayar da kan mazauna karkara da lungunan Nijeriya da kuam sauran duniya game da irin ukubar wannan cuta, da irin ta'adin da take yi, musamman a kasashen Afirka.

An gudanar da wadannan tarurruka ne a garuruwan Lafia, Jihar Nassarawa; da Billiri a Jihar Gombe da kuma Kachako a Jihar Kano.

Dubban masu sauraro sun halarci wadannan tarurrukan, kuma Sashen Hausa yana ci gaba da watsa abubuwan da suka gudana a wurin a kin shirin Karamin Sani wanda ake gabatarwa kowace ranar asabar da misalin karfe 7 na yamma agogon Nijeriya.

XS
SM
MD
LG