Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakiyar Sakataren Tsaron Amurka Ta Ce Ba Su da Shaidar Cewa Akwai 'Yan Al-Qa'ida A Nijeriya


Mataimakiyar sakataren tsaron Amurka mai kula da harkokin Afirka, Theresa Whelan, ta ce Amurka ba ta ga wata shaidar cewa akwai 'ya'yan kungiyar al-Qa'ida a Nijeriya ba.

Amma kuma a cikin hirar da ta yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Ms. Whelan ta ce a cikin Nijeriya akwai 'yan tsagera, wadanda ita kanta gwamnatin Nijeriya ta sansu, wadanda kuma suke tausayawa akidoji irin na al-Qa'ida, har ma ta ce tana yiwuwa wadannan 'yan Nijeriya suna da hulda ko kuma dangantaka da kungiyar al-Qa'ida ko kuma kungiyoyi masu ra'ayi irin nata.

Dangane da batun rahoton da Majalisar Kula da Ayyukan Leken Asiri ta Kasa ta Amurka ta bayar cewa Nijeriya zata iya wargajewa a cikin wasu 'yan shekaru, mataimakiyar sakataren tsaron Amjurka ta ce a can baya, an sha yin hasashen cewa Nijeriya zata wargaje, amma kuma kasar ta buwayi tunanin irin wadannan mutane kuma ta ci gaba da kasancewa a zaman kasa.

Ms. Whelan ta ce ab ta son at shiga sahun masu hasashen cewa Nijeriya zata wargaje, amma kuma irin matsalolin cikin gida dake damun Nijeriya sun yi matukar yawa, kuma idan har ba warware su aka yi ba, to zasu iya gurgunta kasar.

Da ta juya kan batun irin goyon bayan da Amurka take samu daga kasashen Musulmi a Afirka, Ms. Whelan ta ce kokarin da suke yi shine na tabatarwa da mutanen wadanan kasashe cewar su ba abokan gabar Musulunci ba ne, shi ya sa ma sukeada dukkan ayyukan soja da suke gudanarwa tare da ayyukan agajin jinkai.

XS
SM
MD
LG