Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tandja Mamadou ya Yaba Da Yafewa Nijar Bashin Da Aka Yi


Tandja Mamadou
Shugaba Tandja Mamadou na Jamhuriyar Nijar yayi kira ga manyan kasashe masu bin tafarkin dimokuradiyya a fadin duniya da su tallafawa kasashen dake rarrafe a fagen kafa mulkin dimokuradiyya ta yadda za a samu dorewar wannan tafarki da nufin kara arzikin jama'a.

A cikin hira ta musamman da shugaban na Jamhuriyar Nijar yayi da Sashen Hausa na Muryar Amurka a birnin Washington, ya ce tabbatar da dorewar mulkin dimokuradiyya a kasa maras galihu kamar Nijar yana da matukar wuya, kuma ya ce shi da 'yan'uwansa shugabannin da suka gana da shugaba George W. Bush na Amurka sun fada masa bukatar dake akwai ta samun tallafi domin dorewar irin wannan mulki.

Shugaba Tandja ya godewa kasashen duniya masu arzikin masana'antu wadanda suka yafewa jamhuriyar Nijar da wasu kasashe 17 basussukan da ake binsu, yana mai fadin cewa wannan kudi da ya kamata a ce sun biya bashin da shi, zasu karkata shi zuwa ga ayyukan raya karkara a duk fadin Nijar.

Sai dai kuma shugaban na Nijar ya roki kasashen duniya da kada su rufe kofar bayar da bashi nan gaba ga Nijar ko wadannan kasashe, da yake ya ce tilas ne su bukaci agajin raya kasa nan gaba.

Dangane da batun yunwar da ake fama da ita a wasu sassa na Jamhuriyar Nijar, shugaba Tandja Mamadou ya ce suna kokarin sayo abinci, tare da hadin kan gwamnatocin yankin Afirka ta yamma da kungiyoyin kasa da kasa masu zaman kansu, domin saidawa cikin rahusa ga jama'a, yana mai fadin cewa bala'in farin dango da aka fuskanta a bara da kuma kwamfan ruwa, sune suka haddasa wannan lamarin.

Domin jin cikakken bayanin da shugaba Tandja Mamadou yayi, sai a taba rubutun dake can sama domin a saurari cikakkiyar hirar da yayi da Ibrahim Alfa Ahmed.

XS
SM
MD
LG