Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Flying Eagles Na Nijeriya Sun Dirkaki 'Yan Netherlands Masu Masaukinsu


'Yan Flying Eagles na Nijeriya suna murnar jefa kwallo
'Yan wasan Flying Eagles na Nijeriya, tare da mai koyar da su wasa, Samson Siasia, sun yi kudu zuwa Kerkrade daga birnin Doetinchem, inda suka yi waje-rod da 'yan wasan kasar Ukraine da ci daya da babu (1-0) a zagaye na biyu na wasan cin kofin kwallon kafar matasan duniya da ake yi a Netherlands.

A yanzu, Samson Siasia da yaransa sun kwallafa idanunsu a kan masu masaukin baki, Netherlands, wadanda zasu gwabza da su ranar asabar a birnin Kerkrade.

Mutane kalilan suka zaci cewar Nijeriya zata haye zagayen farko daga rukunin da aka ce shine mafi karfi a gasar, rukunin da ya hada har da kasar Brazil dake rike da kofin a yanzu. Haka kuma mutane 'yan kalilan suka zaci cewa Nijeriya zata iya doke 'yan wasan Ukraine a zagaye na biyu a saboda yadda Ukraine ta ringa kai maza kasa a zagayen farko.

Amma kuma a saboda yadda 'yan wasan Flying Eagles suke taka tamaula a aman kungiya guda, ga kuma mashahurin dan wasan da ya zamo mai koyarwa, Samson Siasia, 'yan Flying Eagles sun danne, suka kuma bankade 'yan Ukraine.

Taye Taiwo, wanda dan vwasan baya ne, shi ne ya jefa wa Nijeriya kwallonta guda da ya zamo bambanci a wanan wasa a cikin minti na 80.

Shi kuma Sani Kaita da Olubayo Adefemi wanda ya shiga daga baya, sun yi kirif suka rufe kofa, suka hana shahararren dan wasan Ukraine, Oleksandr Aliiev, sakat.

A yanzu 'yan Flying Eagles zasu gwabza da 'yan wasan Netherlands wadanda suka doke kasar Chile da ci uku da babu (3-0). Shahararren dan wasan Netherlands mai bugawa kungiyar Ajax Amsterdam, Ryan Babel, ya jefa kwallo guda, ya taimaka wajen jefa guda.

A sauran wasannin kwata-fainal da za a yi kuwa, Argentina, wadda sau hudu tana lashe wannan kofi, zata kara da Spain wadda ta doke Spain da ci uku da babu (3-0). Ita Argentina ta doke Colombia ne da ci biyu da daya (2-1).

Daya kasar Afirka da ta rage, Morocco, zata kara da Italiya, Jamusawa kuma zasu kece raini da 'yan Brazil.

XS
SM
MD
LG