Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Garang Ya Zamo Mataimakin Shugaban Kasar Sudan


John Garang
An rantsar da tsohon madugun ’yan tawayen Sudan, John Garang, a zaman mataimakin shugaban kasa, a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kawo karshen yakin basasar shekaru 21 a kasar.

A wajen wani bukin da aka yi yau asabar a Khartoum, babban birnin kasar, Mr. Garang ya zamo mutum na biyu wajen girma a bayan tsohon abokin gabarsa Omar Hassan al-Bashir.

Mr. Garang ya ce kasancewarsa a babban birnin alama ce ta zahiri cewar an kawo karshen yakin basasa. Wannan shi ne karon farko da Mr. Garang ya sanya kafa a Khartoum a cikin shekaru 22.

Daga cikin wadanda suka halarci bukin na yau asabar har da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, da mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka, Robert Zoellick.

A bayan zamowa mataimakin shugaban kasa, Mr. Garang zai shugabanci gwamnati mai kwarya-kwaryar ikon cin gashin kai a kudancin kasar. A wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyar, ’yan kudancin Sudan zasu jefa kuri’a cikin shekaru 6 a kan ko zasu ci gaba da zama a karkashin Sudan, ko kuma zasu balle su kafa kasarsu dabam.

XS
SM
MD
LG