Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Zata Ninka Agajin Abincin Da Take Bayarwa ga Al'ummar Nijar


Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar samar da agajin abinci na gaggawa ga mutanen da suka ninka kiyasinta na farko har sau uku a Jamhuriyar Nijar, a saboda a wani bangare, masu bayar da agaji su na jan kafa wajen takalar matsalar yunwa dake addabar kasar.

A yau talata jami'an Hukumar Abinci ta Duniya suka yi rokon da a ba su karin agajin dala miliyan 12 domin su samar da abinci ga mutane miliyan daya da dubu dari biyu. Suka ce yunkurin farko da hukumar ta yi na magance matsalar karancin abinci a Nijar ya fuskanci cikas a saboda rashin samun kudi da wuri, da kuma wuyar da ake fuskanta wajen sayen abinci a kasashen yankin.

Hukumar ta ce kudin da ta roka a cikin watan Mayu domin ciyar da mutane fiye da dubu 450 a Nijar bai shiga hannunta ba sai a cikin makonni shidan da suka shige.

Jamhuriyar Nijar tana fuskantar kwamfan ruwa mafi muni da ta gani cikin shekaru da yawa, ga kuma illar mamayen farin dango.

XS
SM
MD
LG