Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton Yana Kokarin Samar Da Magungunan Kanjamau Ga Yara A Kasar Kenya


Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, yana kokarin samar da magunguna masu dakushe kaifin kanjamau ga daruruwan yaran dake fama da wannan cuta a kasar Kenya.

A yau asabar ne Mr. Clinton da ministar kiwon lafiya ta Kenya, Charity Ngilu, suke kaddamar da shirin Samar da Magunguna ga yara masu fama da cutar kanjamau a asibitin Mbagathi dake Nairobi.

Wannan shirin zai samar da magungunan dakushe karfin kwayoyin cutar HIV ga yara dubu daya. Wannan adadi kuwa daidai yake da yawan yaran dake samun irin wadannan magunguna a yanzu haka a kasar Kenya.

Gidauniyar Mr. Clinton ta ce yara dubu 100 ne suke fama da cutar kanjamau a kasar Kenya.

Tsohon shugaban na Amurka yana rangadin kasashe 6 a nahiyar Afirka domin nazarin shirye-shiryen yaki da cutar kanjamau da gidauniyarsa ta kirkiro. Tuni ya ziyarci kasashen Mozambique, Lesotho, Tanzaniya, da Afirka ta Kudu. Daga Kenya kuma zai zarce zuwa Rwanda.

A jiya jumma’a Mr. Clinton yayi jawabi gaban ’yan jarida tare da shugaba Mwai Kibaki na Kenya inda ya tabo batun tsarin mulkin dimokuradiyya.

XS
SM
MD
LG