Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Britaniya Sun Ce Mutumin Da Aka Harbe A Tashar Jiragen Karkashin Kasa Ba Ya Da Wata Alaka Da Hare-Haren Bam


Hukumomin Britaniya sun ce mutumin nan da 'yan sanda suka harbe suka kashe a wata tashar jiragen karkashin kasa jiya jumma'a, ba ya da wata alaka da hare-haren da aka kai cikin 'yan kwanakin nan a wasu hanyoyin sufuri an London.

A cikin wata sanarwar da ta bayar a yau asabar din nan, hukumar 'yan sanda ta Britaniya da ake kira Scotland Yard, ta bayyana harbe wannan mutumi a zaman kuskure babba, kuma abinda 'yan sanda na birnin London suka ji takaicinsa ainun.

Jami'ai suka ce ana bin sawun mutumin ne dangane da yunkurin da aka yi na kai hare-haren bama-bamai ranar alhamis, ya kuma ki bin umurnin da 'yan sanda suka ba shi na ya tsaya a lokacin da yake gudu a cikin wata tashar dake karkashin kasa.

Shaidu sun ce 'yan sanda masu fararen kaya sun bi wannan mutumi mai kama da jinsin Asiyawa zuwa cikin wani taragun jirgi, suka kuma harbe shi kusa da kusa.

Wannan al'amari ya faru a daidai lokacin da aka kaddamar da wani gagarumin farauta na mutanen da suke da hannu a hare-haren da aka yi yunkuri a cikin ababen sufurin jama'a na London ranar alhamis. Hukumomi sun ce su na ci gaba da yin tambayoyi ma wasu mutane biyu da aka yi imanin su na da hannu a hare-haren.

A halin da ake ciki, kwararru sun ce binciken kimiyya da kuma lokutan kai hare-haren makonni biyu daidai a bayan na ranar 7 ga watan Yuli inda aka kashe mutanr 56, sun nuna cewar kungiyar 'yan ta'adda guda ta shirya kai hare-haren.

XS
SM
MD
LG