Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Thabo Mbeki Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike


Shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu ya bukaci da a gudanar da bincike dangane da rade-radin cewa shi da wasu ne suka kulla makarkashiyar birkita ayyukan siyasar tsohon mataimakinsa, Jacob Zuma.

A cikin wata wasikar da aka buga jumma’a a kan dandalin jam’iyyar ANC a duniyar gizo, Mr. Mbeki ya nuna fusatarsa da zargin da wasu ke yi a cikin jam’iyyar cewar shi da wasu suna kokari ne su hana Mr. Zuma zamowa shugaban kasar.

A cikin watan Yuni Mr. Mbeki ya kori Mr. Zuma, wanda ke da farin jini matuka a idanun ’yan jam’iyyar, jim kadan a bayan da aka tuhumi mataimakin nasa da laifin zarmiya. Wannan tuhuma kuwa ta biyo bayan da aka samu babban mashawarcin Mr. Zuma kan harkokin kudi da laifin zarmiya da cin hanci a wasu harkoki masu alaka da shi mataimakin shugaban.

Mr. Zuma ya musanta tuhumar da ake yi masa.

A cikin wasikarsa ta jiya jumma’a, shugaba Mbeki ya ce bai kamata a ringa zaton wani dan jma’iyyar ANC da wata boyayyiyar manufar siyasa ba.

XS
SM
MD
LG