Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwar Teku Mai Suna Katrina Ta Yi Barna Mai Yawan Gaske A Jihohin Dake Gabar Tekun Mexico A Amurka


Shugaba Bush ya katse hutunsa, kuma yana shirin komowa Washington domin sanya idanu a kan kokarin da gwamnatin tarayya keyi na taimakawa mutanen da suka tagayyara a sanadin mahaukaciyar guguwar teku mai suna Katrina.

Shugaba Bush zai komo Washington larabar nan, kwanaki biyu kafin hutunsa ya kare domin sanya nidanu a kan ayyukan farfadowa a jihohin dake gaba da tekun Mexico, wadanda mahaukaciyar guguwar ta yi wa kaca-kaca.

Shugaba Bush ya ce Amurkawa suna taya mutanen yankin addu'a, yana mai fadin cewa, "wannan mawuyacin lokaci nne ga mutanen wadannan jihohi. Mun san cewa da yawa sun kosa su koma gidajensu, sai dai hakan ne ba zai yiwu a wannan lokaci ba."

Mr. Bush ya ce a yanzu abu mafi muhimmanci shi ne na ceto rayukan mutane, inda ya lura da cewa a yanzu haka ma'aikatan agaji suna kokarin ceto mutane. Ya ce an tura ma'aikata da kayan aiki, kuma su nna kokarin taimakawa jama'a.

Shugaban na Amurka ya ce, "Gwamnatocin btarayya, jihohi da kananan hukumomi su na aiki tare domin taimakawa mutane su farfado su nniya twsayawa kan kafafunsu, kuma akwai aiki agabanmu."

Shugaban ya bayyana wannan a wani jawabin da yayi gaban sojoji a San Diego a Jihar California. Da farko ya shirya komawa gidan gonarsaa a Jihar Texas domin karasa hutun da yake yi. Amma a maimakon haka, wani kakaki ya ce zai koma gidan gonar ya kwana, sai ya komo Washington larabar nan.

A halin da ake dciki dai an bayar da rahoton cewa irin barnar da mahaukaciyar guguwar teku ta Katrina ta yi zata iya haura ta dala miliyan dubu 26, abinda zai sanya ta ta zamo bala'i guda mafi muni a duk tarihin Amurka.

Tuni an tabbatar da mutuwar mutane fiye da 70, yayin da ake kyautata zaton yawansu zai karu. Wata kunyar dake tare wani tabki a birnin New Orleans kuma an ce ta karye, kuma a yanzu haka kusan dukkan gidajen dake birnin suna karkashin ruwa, akasarinsu ba a ganin komai su rufinsu.

XS
SM
MD
LG